Zamfara: ‘Yan Bindiga Sun Kaddamar Da Kona Ofisoshin ‘Yan Sanda

Labarin dake shigo mana daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar wasu ‘yan bindiga su kai wani hari inda suka kona ofishin ‘yan sanda da gidaje a ƙauyen Zugu na ƙaramar hukumar Bukkuyum dake Jihar.

Sai dai wani shugaban matasa a Bukkuyum ya shaida cewa babu wanda ya rasa ransa a sanadiyar harin kawo yanzu.

Ya kara da cewa mazauna yankin sun tsere daga kauyukansu zuwa garin Bukkuyum da wasu ƙauyukan da ke cikin ƙaramar hukumar Gummi mai makwabtaka domin neman mafaka daga hare-haren.

Sai dai kakakin rundunar ‘yan sanda a Jihar Zamfara Mohammed Shehu, bai amsa kiran da manema labarai suka yi a sa ba kan harin na ƙauyen Zugu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply