Za A Kaddamar Da Littafin Tarihin Aisha Buhari

Rahotanni daga fadar Shugaban kasa na bayyana cewar tuni shiri ya yi nisa wajen kaddamar da wani littafin da aka rubuta a game da uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari.

A lokacin da Mai dakin shugaban kasar ta dawo Najeriya daga kasar tarayyar Larabawa, UAE, ana shirin kammala shirye-shiryen kaddamar da wannan littafi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa abin da ya rage shi ne ayi bikin kaddamar da littafin a fadar shugaban kasa na Aso Villa ranar Juma’a da karfe 9:00 na safe.

Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, shi ne zai shugabanci wannan taro da za ayi.

Attajirar nan, Folorunsho Alakija, ita ce babbar bakuwar ranar. Aliko Dangote, Abdusamad Rabiu, Prince Authur Eze, Hajiya Bola Shagaya, Femi Otedola, Tony Elumelu, su na cikin manyan attajiran da za su halarci taron.

Manyan kasa da aka gayyata wajen bikin su hada da; Sarkin Ife, Adeyẹ́yẹ̀ Ẹnitan Ògúnwusi; Sultan Muhammadu Sa’ad Abubakar III da Mai martaba Appolus Chu.

Har ila yau surukin Buhari, Mohammadu Indimi, da Jim Ovia, Kessignton Adebutu, Daisy Danjuma, Idahosa Wells Okunbo duk za su samu halartar bikin.

Ministocin da za su bada masaukin baki su ne Ministan babbar birnin tarayya, Mohammad Bello da takwararsa, Ministar harkokin mata ta kasa, Pauline Tallen.

Dr. Hajo Sani ce ta rubuta wannan littafi da babban malami, Farfesa Fatai Aremu ne ya yi wa ta’aliki.

Labarai Makamanta