‘Yan Ta’adda Sun Kashe Fulani Sama Da Dubu 10 A Najeriya – Miyyeti Allah

Ƙungiyar kare al’adun Fulani a Najeriya ta Miyetti Allah ta ce an kashe makiyaya aƙalla 10,000 tare da raba wasu miliyan biyu da muhallansu a faɗin ƙasar cikin shekara bakwai da suka wuce.

Bayanan sun fito ne bayan wani taro kan tsaro da ƙungiyar ta shirya tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Northern Consensus Movement (NCM) ta ‘yan Arewa sakamakon matsalolin tsaro da suka ce Fulani na fuskanta, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito ranar Asabar.

Cikin wata sanarwar bayan taro a ranar Juma’a, ƙungiyar ta ce daga 2015 zuwa yanzu makiyaya da dama sun fuskanci matsaloli, inda aka sace ko kashe dabbobi fiye da miliyan huɗu.

“Yi wa Fulani baƙin fenti da nuna musu tsana da kuma rura wutar ƙabilanci a kan su da kafofin yaɗa labarai ke yi ka iya kaiwa ga kisan ƙare-dangi,” in ji sanarwar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply