Sunusi Alheri Ne A Najeriya – Shugabannin Tijjaniya

An bayyana tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II a a matsayin wani haske kuma tauraro wanda samun shi a Najeriya ke matsayin wata samun nasara ga kasar, wannan shaida ta fito ne daga bakin Shugabannin darikar Tijjaniyya inda suka bayyana tsohon Sarkin Kano, Mohammadu Sanusi II shugaban Tijjaniya alheri ga Najeriya.

Malaman da suka bayyana hakan lokacin da suka kai ziyarar ban girma gidansa na Kaduna sun kuma ce duk mabiyansu a Najeriya da Afirka suna alfahari da shi.

Wakilin shugaban darikar Tijjaniyya na duniya, Sheikh Abdul-Ahad Nyass wanda ya jinjinawa tsohon sarkin ya ce shawara ce ta bai daya da kasancewar tsohon sarki sanusi a matsayin Khalifa a Najeriya.

Ya kara da cewa shugaban darikar Tijjaniyya na duniya Sheikh Mahi Nyass yana alfahari da nasarorin da tsohon sarki ya samu a rayuwar jama’a da kuma a matsayin masarauta.

Ya bayyana babban taron da mabiyansu suka yi zuwa Kaduna don karrama Sanusi, a matsayin shaidar yadda tsohon sarkin har yanzu ya ke da karbuwa da girma a idon mutane wadanda ke da cikakken kwarin gwiwa kan halayen jagorancinsa.

Har ila yau, Sheikh Mukhtar Adhama ya bayyana imanin cewa Sanusi a matsayin Khalifan darikar Tijjaniyya zai karfafa koyo da zurfafa ilimi a tsakanin mabiyansu.

A jawabinsa, tsohon sarki Sanusi ya tuna cewa tun kafin ya hau karagar mulki a Kano, ya ziyarci manyan Shehunai na Tijjaniyya a Kaulaha ta kasar Senegal wadanda suka yi addu’a kuma suka yi hasashen cewa zai zama sarkin Kano.

Ya tuna cewa hatta shugabancin da Tijjaniyya ta daura masa a yanzu, 80% na wadanda suka amince da shi Shehunai ne da bai san su ba. Daga karshe ya yi addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya tare da gargadin ‘yan kasar da su zama masu hakuri da bin doka da oda.

Labarai Makamanta

Leave a Reply