Najeriya Za Ta Gyaru Idan An Kawar Da Wasu Mutane – Al-Mustapha

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar tsohon dogarin marigayi shugaban kasa na mulki Soja, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya bayyana cewa wasu mutum 56 ke hana ruwa gudu a Najeriya.

Al-Mustapha yace wadannan mutane 56 ke cinye arzikin Najeriya. Ya bayyana cewa lokacin da yake daure, yayinda ake azabtar da shi ya fahimci wadannan mutane 56 kuma idan aka samu nasarar kawar da su, Najeriya za ta samu cigaba.

Al-Mustapha ya bayyana hakan ne yayin hira da sashen Hausa na BBC a birnin tarayya Abuja.

Labarai Makamanta

Leave a Reply