Kofata A Bude Take Ga Duk Mai Bukatar Aure Na – Fati Gwammaja


Fitacciyar jaruma a cikin shirin Kwana Casa’in Fati Gwammaja wacce aka fi sani da Amina matar Sambo, ta yi kira ga mata abokan sana’ar ta na fim cewar, lallai su rinka kiyaye duk wata mu’amala da suke yi da jama’a, saboda gudun abin da zai bata musu suna.

Jarumar ta bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya, dangane da irin Matsalolin da a ke kallon mata suna haifar wa, a cikin masana’antar fina-finai ta Kannywood.

Jarumar ta ce “Abin da zan yi kira a gare mu mata masu harkar fim har da ni shi ne, lokaci ya yi da za mu san cewa,duk wanda ya fitar da fuskar sa duniya ta san shi. To hankalin mutane yana dawowa kan shi ne, don haka sai mun rinka taka tsan tsan da rayuwar mu, domin da wani zai zo ya nuna yana son mu” inji ta.

“Don haka sai mun rinka kiyaye wa musamman a game da Video Call. Domin yana daya daga cikin abin da ya ke sakawa mu samu Matsaloli, kina gida a kwance sai a kira ki Video Call ki daga ba tare da kin kula da yanayin da kike ciki ba, to wannan ya kan sa idan abin ya fito sai a samu matsala, don haka jarumai a rinka kiyayewa, don gudun abubuwan da za su jawo mana matsala. ”

Ko da muka yi mata maganar aure kuwa cewa ta yi, “Aure ina jiran sa duk lokacin da Allah ya kawo mun don haka idan za ka fada, fadi Ka Kara, ni yanzu a kasuwa nake, ina fatan Allah ya kawo mun miji nagari.” a cewar ta

Labarai Makamanta