Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutane 29 Da Aka Yi Safararsu Zuwa Waje

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina, karkashin jagorancin kwamishinan’yan sanda Alhaji Sanusi Buba, ta yi nasarar cafke wadansu matasa maza da Mata guda ashirin da tara, daga kudancin Nijeriya.

Domin yin safarar su zuwa Kasashen wajen domin neman kudi da bauta a kasashen Libya da Aljeriya da kuma Turkiyya.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Katsina, SP Gambo Isa ya bayyanawa manema labarai su. Inda ya ce an kama su ne suna niyyar ficewa a garin Unguwar Dan jummai da ke cikin karamar hukumar Mai’adua a jihar Katsina, wanda garin yana Kan iyaka ne tsakanin Nijeriya da jamhuriyar Nijar.

A cikin su akwai Mata ashirin da biyu da maza biyar da kananan yara biyu. Ana ci gaba da bincike.

Labarai Makamanta

Leave a Reply