Duk Wanda Ya Riki Al-Kur’ani Ba Zai Tabe Ba – Sheikh Dahiru Bauchi

Daga Adamu Shehu Bauchi

Shahararren Malamin nan Sheikh Dahiru Usman Bauchi yaja hankalin Iyaye da yayansu su riki Alkur’ani Mai Girma ta wajen haddace shi da Kuma sanin abinda yake koyarwa don samun al’umma mai inganci da kuma Ladan da bashi da iyaka a wajen Allahu subahanahu-wata’ala.

Shaihin Malamin yayi wan nan Jan hankalin ne a lokacin da yake dana Uwar gidan Gwamnan Jihar Bauchi Hajiya Aisha Bala Mohammed a matsayin Garkuwar masu haddan Alkur’ani ta Jihar Bauchi a fadar gidansa tare da jikan Manzon Allah (S.A.W) a kusa dashi a gidansa dake garin Bauchi.

Dahiru Bauchi, ya Kara da cewa wan nan sarautar da ya baiwa Uwar gidan Gwamnan shine yafi kowane irin sarauta da tasa mu a dukkan tsawon rayuwarta, saboda haha yace tayi hattara da Kara kwazo akan ayyukan ta na alheri ga jama’ar Jihar baki daya.

San nan ya kara da cewa wan nan rana Yana da muhimanci a gareshi da ita da mutanen Bauchi baki daya, a adaidai lokacin da ake gudanar da wan nan bikin, sai ga Jikan Manzon Allah (S.A.W) Sheikh Ali Sharif Bin Arabi, shima ya iso wan nan wuri da tawagarsa a ziyarsa da ya kawo Jihar Bauchi, daga kasar Aljeriya, saboda haka yace ta godewa Allah da wan nan babban rabo da tasamu.

Har, ila yau a wajen taron ya gargadi Shuwagabanni na siyasa a Najeriya da su daina fada da makaranta Alkur’ani da masu haddace shi, in basu naso so jawo wa kansu bala’i ba ne, yace hakan ba daidai koma bashi da kyau ko Kan kani

Ana ta jawabin jim kadan bayan an nada ta Uwar gidan Gwamna Hajiya Aisha Bala, tasha alwashin tallafa ma masu son karo karatu ta fannoni dabam dabam a makarantar Gidauniyar Amuhibbah dake garin Abuja wacce itace ta kafa wan nan makarantar gidauniyar don amfanan al’umma n Bauchi da ma Najeriya baki daya.

Ta kara da cewa, tana yiwa Allah godiya da aka nada ta a matsayi irin wan nan, na garkuawan mahaddata Alkur’ani mai Tsarki, tace hakika zatayi amfani da wan nan dama da ta samu ta hanyar da ya dace.

Daga karshe anyi addu’oin zaman lafiya a Jihar Bauchi da Najeriya baki daya,

Labarai Makamanta

Leave a Reply