Dakarun Soji Sun Kakkabe Sansanin Boko Haram

Labarin dake shigo da Hedikwatar tsaro ta ƙasa na bayyana cewar domin cika umarnin Shugaban ƙasa Buhari na kawar da dukkan yan bindiga da yan ta’adda da ke adabar yankunan arewa jirgin yakin Sojin saman Najeriya NAF da sojoji sun kashe yan ta’adda fiye da 85 a jihohin Borno, Zamfara, da Kaduna a hare haren da suka kai.

Sojojin Saman Najeriya sun kai hare-hare a dajin Sambisa ta Jihar Borno da Sangeko a Zamfara da dajin Kusasu a Jihar Kaduna inda suka kashe fiye da yan ta’adda 150.

Kakakin rundunar Sojin Saman Najeriya NAF ya tabbatar da kai harin amma ya ce makasudin atisayen shine kara ragargazan yan ta’adda da ke arewa maso gabas da arewa maso yamma, da nufin samar da zaman lafiya a yankin.

Majiyoyi daga rundunar soji wanda suke cikin wadanda suka kai harin sun ce a Zamfara, dakarun Operation Hadarin Daji sun yi ruwan bama-bamai a dajin Sangeko, hakan yasa aka kashe kimanin yan ta’addan 50 da aka hange su kan babura suna shirin kai hari.

Bayan tabbatar da wurin taron yan ta’addan da fasahar ISR, an umarci jirgin yakin NAF ya kai hari a wurare daban-daban tare da wasu jami’an tsaro. Hakazalika, an sake yi wa yan ta’addan da aka hangi suna tserewa daga harin na farko ruwan wuta, an kawar da su.

A dajin Kusasu, binciken da NAF ta yi da na’urar ISR daga ranar 30 zuwa 31 na watan Maris, ya tabbatar da yan ta’addan suna zirga-zirga suna barin dajin a cikin dare.

Labarai Makamanta

Leave a Reply