Da Dumi-Dumi: Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Magaji Rimin Gado

Rahotanni dake shigo mana yanzu haka daga Kano na bayyana cewar Majalisar dokokin Jihar ta dakatar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Jihar Magaji Rimin Gado daga muƙamin shi biyo bayan kememe da ya yi dangane da umarnin da ofishin Akanta Janar na Jihar ya aike mishi.

Wannan ya biyo bayan wata takardar koke da ofishin Akanta Janar ya fitar akan shi wanda aka tura wa Majalisar.

Takardar ta bayyana cewar Magaji Rimin Gado ya dauki mai mataki na 4 a matsayin babban Akanta a hukumar wanda yin hakan ya ci karo da dokokin jihar Kano.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Labaran Madari ya bukaci majalisar da ta hannata batun ga kwamitin bincike na Majalisar domin daukar matakin da ya dace.

Sannan majalisar ta bukaci kwamitin da ya kammala binciken shi da gabatar da sakamakon binciken nan da makwanni biyu masu zuwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply