Buhari Ya Yi Tir Da Harin Da Boko Haram Ta Kai Jihar Adamawa

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhar ya yi tir gami da Allah wadai bisa kisan gilla Boko Haram suka yi wa wasu yan Najeriya da suka haɗa da wani shugaban yan tawagar bijilanti da dagacin ƙauyen Dabna dake ƙaramar hukumar Hong, jihar Adamawa.

Da yake martani kan lamarin, shugaba Buhari yace “Wannan ta’asar, rashin imani, da rashin mutunci ne kuma ɗaukar rayuwar mutane ba zai tafi hakanan ba.

A wani jawabi da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya fitar ranar Alhamis, Buhari ya umarci jami’an tsaro cewa “ku ninka ƙoƙarin da kukeyi wajen ɗaukar mataki a kan wannan barazanar tsaron cikin gaggawa.”

“Ba zamu amince mu baiwa yan Najeriya kunya ba dangane da amanar da suka danƙa a hannun mu na tsare rayuwarsu.” inji shi.

Gwamnati zata tallafawa iyalan waɗanda abun ya shafa, Shugaba Buhari ya umarci hukumomin da abun ya shafa ƙarƙashin jagorancin ma’aikatar jin ƙai da walwala da su gaggauta gano abubuwan da aka rasa a waɗannan yankuna kuma su tura da tallafin gwamnati.

Labarai Makamanta

Leave a Reply