Borno: APC Ta Kafa Kwamitin Sasanci

Jam’iyyar APC a Jihar Borno ta kafa wani kwamiti domin sasanta ƴaƴan jam’iyyar da ke da ƙorafe-ƙorafe bayan zaɓukan fitar da gwanin da aka gudanar a faɗin jihar.

Shugaban jam’iyyar na APC a Jihar Borno Ali Bukar Dalori ne ya ƙaddamar da kwamitin a Maiduguri.

Ya bukaci kwamitin ya ziyarci dukkan ƴan jam’iyyar da suka nemi yin takara a mukamai daban-daban amma ba su gamsu da sakamako zabukan ba.

Baya ga lauya M.T. Monguno da Adamu, akwai kuma Mohammed Makinta, Alhaji Kaumi Damboa, Babagana Malarima, Sani Kuli Askira, Modu Kawu Ngamdu, Babagana Tijjani Banki da kuma Zakari Dali Bayo cikin mambobin kwamitin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply