Zuwan Aisha Dubai Neman Magani Ne – Fadar Shugaban Kasa

Fadar Shugaban kasa ta fito fili ta yi tambihi gami da ƙarin haske akan tafiyar da Uwargidan Shugaban Kasa Aisha Buhari ta yi zuwa Dubai, inda aka bayyana cewar Uwargidan Shugaban ta je Dubai ne domin ganin Likita saɓanin jita-jitar da wasu ke yaɗawa na cewar wai ta yi gudun hijira ne saboda taɓarbarewar tsaro a Najeriya.

A baya can an taba samun lokacin da aka yi watanni Aisha Buhari ba ta fadar Shugaban kasa Villa, wanda hakan na da nasaba da batun duba lafiya da ta saba zuwa waje a duba ta, musanman birnin Dubai.

Tun lokacin da Hajiya Aisha Buhari ta fice zuwa birnin Dubai a kasar Tarayyar Larabawa, UAE, ba tare da an ji labari ba, har yau ba ta dawo ba jama’ar Najeriya ke cigaba da yin cece kuce akai.

Wani daga cikin hadiman uwargidar Shugaban Kasar Kabiru Dodo, ya fito ya bayyana halin da ake ciki a karshen makon nan a jihar Taraba.

Malam Kabiru Dodo ya tabbatar da cewar Aisha Buhari ta je ganin Likita ne amma ba wai batun rashin tsaro ya sa Aisha Buhari ta bar Aso Villa ba, yace ta bar kasar ne domin a duba ta.

“Uwargidar shugaban Najeriya ta yi tafiya ne domin ganin likita, ba ta bar Najeriya saboda matsalar rashin tsaro ba.” Inji Kabiru Dodo.

Da manema labarai su kayi yunkurin tuntubar Mai magana da yawun bakin Aisha Buhari, Aliyu Abdullahi, bai iya daukar kiran da aka yi masa ba.

A 2019, Matar shugaban Najeriyar ta yi irin haka, inda ta shafe watanni ba ta gida, bayan ta wuce Ingila, daga nan ta zarce Saudi Arabiya, ta yi Umrah. Idan za ku tuna, a watan Agusta, Aisha Buhari ta fito ta na godewa ‘yan Najeriya da su ka taya ta da addu’o’i yayin da ta ke kwance a gadon asibiti a UAE.

Uwargidan Shugaban kasa A’isha Muhammadu Buhari ta bar gida tun da ta aurar da ‘yarta, Hannan, kafin nan ma ta yi tafiya zuwa kasashen ketare.

Labarai Makamanta

Leave a Reply