Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa, ya bayyana cewa mutum bai da ikon ramawa koda ace dan sanda ya mareshi idan dai har ɗan sandan yana sanye da Inifam.
Olumuyiwa Adejobi, ya ce abin da ya kamata mutum yayi shine ya kai kara gaban hukuma domin doka ta tsawatar masa.
Mai magana da yawun yan sandan ya ce cin mutuncin jami’in dan sanda da ke sanye da kayan aiki tamkar cin mutuncin Najeriya.
Kakakin ‘yan Sandan ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da manema labarai a birnin tarayya Abuja a karshen mako.
You must log in to post a comment.