Zunubi Mafi Girma Na ‘Yan Najeriya Shine Zaɓen Buhari Shugaban Kasa – Yakasai

An bayyana cewar babban kuskuren da jama’ar Najeriya suka yi shine kasadar zaɓen Buhari a matsayin shugaban kasa da suka yi, kuma tabbas ‘Yan Najeriya zasu cigaba da ɗanɗana kuɗarsu yadda ya kamata a tsawon wa’adin shugabancin Buhari na shekaru Takwas.

Dattijon kasa kuma tsohon hadimin tsohon shugaban kasa na tuntuba, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana haka a wata tattaunawa da aka yi da shi, inda ya ƙara da cewar zaben Buhari a matsayin shugaban kasar Nijeriya shi ne babban zunubi da ‘yan Nijeriya suka yi.


Yakasai, wanda ya bayyana haka ne yayin wata hira ta musamman da jaridar Sunday Tribune ta yi da shi, yace a koyaushe ya san cewa shugaba Buhari ba shi da iko da kuma iyawar da zai magance matsalolin Nijeriya.

“Ban taba goyon bayansa ba kuma ba zan goyi bayan Buhari ba. Na san Buhari ba shi da kwarewar da zai iya mulkin kasar nan. Ban taba canza ra’ayina ba game da rashin cancantarsa ​​na shugabancin wannan kasa ba.

Labarai Makamanta