Zulum Ya Bada Tallafin Miliyan 20 Ga Iyalan Marigayi Janar Dzarma

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya jagoranci tawaga zuwa ta’aziyyar marigayi Birgediya Janar Dzarma Zirkushu, wanda ‘yan ta’addan ISWAP suka kashe kwanaki a jihar Borno.

Gwamnan ya gana da iyalan marigayin a sansanin soji na Ribadu dake jihar Kaduna, kuma nan take ya bada umarnin sakin miliyan 20 ga iyalan don tallafa musu.

A wata sanarwa da ofishin gwamna Zulum ya fitar a dandalin Facebook, Kakakin gwamnan, Malam Isa Gusau, yace nan take aka tura musu kudin.

Gusau ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Borno zata tallafawa iyalan sojojin da aka kashe tare da marigayi janar Dzarma Zirkushu.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwa, da kwamandan rundunar soji ta Division One, Birgediya Janar T. Opuene, sune suka tarbi Zulum a filin jirgi.

Zulum ya samu rakiyar sanatocin jihar Borno uku, Kashim Shettima, Mohammed Ali Ndume da Abubakar Kyari; mambobin majalisar dokoki biyu, Dr. Haruna Mshelia da Ahmad Jaha.

Zulum ya gana da iyalan marigayin Gwamnan Zulum ya yiwa matar marigayin ta’aziyya, Blessing Zirkushu, da kuma ƴaƴanta guda 5, bayan ɗan uwan marigayin, Gurdebil Zirkushu, ya tarbe shi da sauran wasu iyalai.

Zulum ya jajantawa iyalan baki ɗaya, kuma ya roke su kada su bar kyakkyawar turbar da marigayi birgediya janar ɗin ya bar musu.

Labarai Makamanta