Labarin dake shigo mana daga birnin Sokoto Daular Usmaniyya na bayyana cewar mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi kira ga al’umma da su dage da Al- Ƙunuti da yin addu’o’i musamman a kan batun rashin tsaro wanda ke addabar Arewa.
Muhammad Sa’ad Abubakar III ya bukaci a dage da yin adduo’in al-kunutu, ganin halin da aka shiga a kasar nan, musamman yankin arewacin kasar inda zubar da jini ya zama ruwan dare.
Sarkin Musulmi ya na so a rika yin wadannan addu’o’i a dukkanin masallatai da dakunan ibada da wuraren zama domin Allah ya kawowa al’umma sauki.
Sakataren kungiyar Jama’atu Nasrul Islam Dr. Khalid Abubakar Aliyu ya fitar da jawabin da Sarkin Musulmin ya yi a karshen Mako.
Jama’atu Nasril Islam ta ce an yi kiran ne saboda ya zama dole a irin wannan yanayi. “Wannan kiran ya zama dole idan aka duba yadda ake ci gaba da kashe rayuka da wulaƙanta su gabagaɗi kamar yadda muka gani a Sokoto da Gidan Bawa da Beni-sheikh da Kaga.”
“Saboda haka ana kiran Musulmi su duƙufa wajen yin alƙunutu a raka’ar ƙarshe ta dukkan sallolin farilla da na nafila domin neman taimakon Allah.”
You must log in to post a comment.