Ziyara Atiku Ya Je Birtaniya Ba Ganin Likita Ba – PDP

“Dan takaran kujerar shugaban kasan Najeriya a zaben 2023 karkashin inuwar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar, ya tafi Landan ne bisa gayyatar gwamnatin Birtaniya ba ganin Likita ba”

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar, Dino Melaye, ya bayyana hakan a ranar Lahadi. Ya yi tsokacin na mayar da martani ga Femi Fani Kayode wanda ya ce an garzaya da Atiku birnin Dubai don jinya.

Ya ce gwamnatin Birtaniya ta gayyacesa ne kamar yadda ta gayyaci Bola Ahmed Tinubu da APC da kuma Peter Obi na Jam’iyyar Labour.

A sakon WhatsApp, Melaye yace: “Ku yi watsi da karerayin makaryata. Atiku na cikin koshin lafiya dari bisa dari.” “Gwamnatin Birtaniya ce ta gayyaci dan takarar kamar yadda ta gayyaci Tinubu da Peter Obi.”

Dino Melaye na cikin wadanda suka yiwa Alhaji Atiku Abubakar rakiya zuwa kasar Birtaniya.

Labarai Makamanta