Zidane Ya Ajiye Aiki Da Real Madrid

Zidane mai shekara 48, ya lashe Champions sau uku a jere a lokaci na farko da yake tafiyar da kungiyar tsakanin shekarar 2016 da 2018.

Ya kuma koma kungiyar inda ya yi watanni 10 kuma ya kammala gasar La Liga a matsayi na biyu.

Tun shekarar 2009-10 rabon da ace Real ta gaza cin kofi ko daya a tarihi.

Tun da wuri aka cire ta daga gasar Copa del Rey, kuma wata kungiya ce da ke buga matsayi na uku a Sifaniya Alcoyano ce ta cire ta.

A kuma gasar zakarun Turai kuma Chelsea ce ta cire Real a matakin wasan daf da na karshe.

“Zidane na daya daga cikin manyan ‘yan wasan Real Madrid da suka cimma tarihi a kungiyar, kuma ya kara fadada nasarorinsa a kungiyar lokacin da ya zama kocin kungiyar” a sanarwar da kungiyar ta fitar.

” Ya san cewa yana cikin zuciyoyin magoya bayan Real Madrid kuma ko da yaushe Real Madrid gida ce a wurin shi.”

A farkon wannan watan ne Zidane ya musanta rahoton da ke cewa ya shaida wa ‘yan wasansa cewa zai bar kungiyar a karshen wannan kakar.

Maganar zamansa a kungiyar ce ta mamaye jaridun Sifaniya, wanda suka ba da gudun mawar kawo sauye-sauye, kan cewa shi da ‘yan wasansa na bukatar girmamawa ta musamman.

Shi ne kadai kocin da ya taba cin Champions sau uku a jere, cikin kuma kofinan da ya ci sun hada da: kofin kwararrun na duniya, da Super Cup biyu da kuma Super Cup na Sifaniya biyu.

Daga ƙarshe dai Kocin na Ƙungiyar Real Madrid ya tabbatar da ajiye aiki da shahararriyar Ƙungiyar kwallon kafa ta nahiyar Turai.

Labarai Makamanta