Zargin Tsafi: An Damke Sanata Ekweremadu A Birtaniya

Rahoton dake shigo mana daga birnin Landan na ƙasar Birtaniya na bayyana cewar Hukumomi a kasar sun damke tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ike Ekweremadu, da matarsa Beatrice kan laifin kai wani yaro kasar don cire wani sashen jikinsa.

Hukumar ‘yan sandan kasar ta tabbatar da labarin cewa an garkamesu a kurkuku kuma za’a gurfanar da su a kotu ranar Alhamis bayan gudanar da bincike, kamar yadda jaridar Skynews ta ruwaito.

‘Yan sandan sun kara da cewa an kaddamar da bincike ne bayan sanar da su wasu sun kawo Yaro dan wata kasa ba bisa ka’ida ba kuma hakan ya sabawa dokar bautar zamani na Birtaniya.

Jawabin yace: “Beatrice Nwanneka Ekweremadu, 55 (10.9.66) ta Najeriya ana tuhumarta da sufarar wani yaro da niyyar cire wani sashen jikinsa.” “Ike Ekweremadu, 55 (10.9.66) na Najeriya ana tuhumarsa da sufurin wani yaro da niyyar cire wani sashen jikinsa.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply