Zargin Ta’addanci: PDP Ta Bukaci A Kori Pantami

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, ta roƙi hukumar tsaro ta farin kaya DSS, da su gaggauta gayyatar ministan sadarwa, sheikh Isa Pantami, domin ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa na goyon bayan Ƙungiyoyin ta’addanci, sannan da ɗaukar matakan da suka dace a kanshi.

Hakanan kuma jam’iyyar ta ba shugaba Muhammadu Buhari shawara a kan ministan, tace yakamata ya kula sosai da wannan lamarin, ba abin wasa bane matuƙar zargin ya tabbata to a gaggauta ɗaukar matakin da ya dace.

Jam’iyyar ta PDP ta bayyana matsayarta ne a wani jawabi data fitar ɗauke da sa hannun kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan , ranar Lahadi kuma aka rarraba ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Kola Ologbondiyan yace: “Jam’iyyar mu ta damu matuƙa da lokacin da ake ɗauka kan wannan lamarin da kuma jayayya da ministan sadarwa, wanda keda ajiyayyun bayanan gwamnati, da bayanan wasu ɗaiɗaikun mutane masu ƙima.”

“PDP ta damu matuƙa da zargin da mutane ke masa, kuma muna gudun kada ministan ya yi abinda bai dace ba wajen ba wasu daba ‘yan ƙasa ba dama suzo su mamaye rijistar NIN ɗin da ake yi yanzun, su zama yan ƙasa.”

Jami’iyyar ta PDP na kira ga DSS su gudanar da bincike kan zarge-zargen, wanda ya jawo cece-kuce da tsoro sosai musamman ma saboda ƙaruwar hare-haren yan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci aƙasar nan.”

Sai dai a ƙarshen makonnan minista Pantami yace bai taɓ zama mai tsattsauran ra’ayi ba kuma shi baya kan wasu maganganu da yayi a baya. Ya kuma ce babu wani malamin addinin musulunci a baya ko a yanzun da ya ƙalubalanci ayyukan Boko Haram kamar shi.

Pantami ya faɗi haka ne a lokacin gudanar da tasirin watan Ramadana da yake gudana a masallacin An-Noor, Abuja.

Labarai Makamanta