Zargin Ta’addanci: Amurka Ba Zata Hana Pantami Biza Ba

An ruwaito cewa tsohon Jakadan Amurka a Najeriya Campbell ya ce gwamnatin Amurka ba za ta iya hana ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali-Pantami bizarta ba, bisa lamari na zargi kawai.

Tsohon jakadan ya ce hudubar Pantami da sauran bayanan da ya yi a bainar jama’a ba za su iya zama mizanin sanya shi cikin jerin yan ta’adda ba.

Campbell, wanda ya yi aiki a matsayin jakada a Najeriya a tsakanin shekarar 2004 zuwa 2007, ya ce wani jami’in ofishin jakadancin zai so sanin lokacin da aka yi wa’azin Pantami da sauran bayanan da yayi a cikin jama’a.

Ya ce: “Har ila yau, akwai tambaya game da ko yana bayar da fatawar tashin hankali ne, ko kuma afuwar da ya nema watsi ne da abunda ya fadi? Shin yanzu yana cikin ƙungiyar ta’addanci ta duniya? Ko kuma, wasu daga cikin ra’ayoyinsa sun yi daidai da na Osama Bin Laden? Kamar yadda kuka sani, ‘yancin faɗar albarkacin baki da tunani na tattare da tsarin Amurka.”

A gefe guda, fadar shugaban kasa ta mayar da martani game da zargin cewa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, ya yi kalamai a baya yana mai goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda. Bayanin fadar shugaban kasar na kunshe ne a cikin jerin sakwannin da babban mai taimakawa Shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Twitter.

Labarai Makamanta