Zargin Sauya Halitta Zuwa Mace: Matar Shugaban Faransa Za Ta Garzaya Kotu

Uwargidan shugaban Faransa, Brigitte Macron, za ta shigar da ƙara kan wani zargin da ake yaɗawa a intanet cewa ta sauya jinsinta zuwa mace bayan an haife ta namiji.

An wallafa labarin ne a wani shafin masu tsauttsauran ra’ayi tun a watan Satumba wanda wasu suka ci gaba da yaɗawa.

Daga cikin masu yaɗawa har da masu adawa da mijinta shugaba Emmanuel Macron da suka ƙunshi masu adawa da rigakafi.

Brigitte Macron tana da ƴaƴa uku manya da ta haifa a aurenta na farko.

A jita-jitar an yi iƙirarin cewa an haife ta namiji ne aka raɗa mata sunan Jean-Michel Trogneux. Sunan ya karaɗe shafukan sada zumunta inda aka ambaci sunan sama da 10,000 a Twitter.

Labarai Makamanta