Zargin Sace Kudin Tallafi: Gwamna Bala Ya Yi Karya – Ma’aikatar Jin Kai

Ma’aikatar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa ta Tarayya ta bayyana wani iƙirari da Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed ya yi cewar wai jami’an gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa sun sace naira biliyan 1 “a kan idon Shugaba Muhammadu Buhari” na Shirin Tallafin Rage Fatara (SIP) wanda ma’aikatar ke gudanarwa da cewar ƙarya ce maras makama.

Wasu kafafen yaɗa labarai sun kuma ruwaito gwamnan ya na faɗin cewa “cin hanci da rashawa ya riga ya ruguza shirin tallafin NSIP na Gwamnatin Tarayya, sannan ya ƙalubalanci gwamnatin da ta kwaikwayi sabon shirin da gwamnatin sa ta ke aiwatarwa a Jihar Bauchi.

Ya yi maganar ne a wajen taron ƙaddamar da shiri mai suna ‘Ƙaura Economic Empowerment Programme

Labarai Makamanta