Zargin Pantami Da Ta’addanci Ƙanzon Kurege Ne – Hadimin Buhari

Hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, ya mayar da martani game da rahotannin da ke cewa Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki, Isa Pantami yana cikin jerin mutanen da kasar Amurka ke zargi da ayyukan ta’addanci.

A daya daga cikin labaranta jaridar yanar gizo ta NewWireNGR ta yi zargin cewa Pantami yana karkashin kulawar Amurka saboda zargin alakarsa da mayakan Boko Haram, Abu Quatada al Falasimi, da sauran shugabannin kungiyar Al-Qaeda.

Ba wadannan kadai ba, jaridar ta yanar gizo ta yi ikirarin cewa Pantami, kafin nadin nasa, sanannen mai wa’azin addinin Islama ne wanda ke yada akida mai hatsari a kan gwamnatin Amurka.

Sai dai kuma, a cikin sakonsa na Twiter a ranar Litinin, 12 ga Afrilu, Ahmad ya yi watsi da ikirarin a matsayin karya, yana mai cewa gidan yada labaran ta cikin gida da gangan ta kauce don tabbatar da gaskiyar lamarin sannan ta ci gaba da yaudarar dimbin makaranta ‘yan Najeriya.

Ya ce: “Yanzu nan kun yada rahoton karya ba tare da tabbatarwa ba. A matsayin ku na kafar yada labarai @NewsWireNGR kun san yadda ake tabbatar da irin wadannan rahotannin, amma a’a, kuna nan kuna yada labarin karya da hadari ga dubban mabiyan ku.Dr IsaPantami bai taɓa kasancewa a cikin jerin mutane da Amurka ke sawa ido ba.”

Labarai Makamanta