Zargin Cin Amana: Shekau Ya Datse Kan Na’ibinshi

Shugaban haramtacciyar kungiyar ‘yan ta’adda na Boko Haram, Abubakar Shekau, ya nada Abu Muhammad a matsayin sabon Amirul Jaysh ‘Kwamandan Yaki’, ga bangaren da yake jagoranta bayan kashe tsohon Kwamandan yaƙin shi Abu Fatimah.

An ruwaito cewa Shekau da kansa ya sa wuka ya datse kan Abu Fatimah, a makon da ya gabata, bisa zargin cin amanar mazhabar su, da ƙoƙarin aiwatar da wasu miyagun abubuwan da suka yi karo da karantarwar Ƙungiyar tasu.

Wata majiya ta bayyana cewa wasu manyan kwamandoji biyu suma ‘Hatsabibi’ Shekau ya kashe su. Majiyar ta kara da cewa “Bayan wani rikici na cikin gida, Shekau ya kashe Abu Fatima, wani Kwamandansa kuma Amirul Fi’ya, wanda da ne ga fitaccen dan kasuwar Bama, Alhaji Modu Katakauma.

Labarai Makamanta