Zanga-Zangar Landan: Masoyan Shugaban Kasa Sun Kunyata ‘Yan Adawa

Bayan wata zanga-zangar ds wasu ‘yan Najeriya da ake zaton ‘yan adawa ne mazauna birnin Landan suka yi wa Shugaban ƙasa Buhari a masaukin shi dake babban birnin kasar, inda zanga-zangar ta rikide wani abu daban ta hanyar zage zage da cin mutunci.

Daga bisani gungun wasu masoya Shugaban kasar a birnin Landan suma sun gudanar da wata zanga-zangar lumana da nuna goyon baya ga Buhari da kuma kishin Najeriya.

Masoya Shugaban kasar sun isa masaukin Shugaban Najeriya dake birnin Landan gidan da aka fi sani da ‘Abuja House’ da takardu masu dauke da rubutu kamar haka ‘Tabbas wannan guguwar za ta wuce’, ‘Allah na son Nijeriya’ da nufin nuna goyon bayansu ga shugaban kasar.

Zanga-Zangar lumana da masoya Buhari suka gudanar tamkar kunyata wadanda suka gudanar da zanga-zangar farko ne ta sukar Shugaban kasar, inda suke nuna cewar ‘yan Najeriya sun dawo rakiyar shugaban.

Masu adawa da gwamnatin Buhari, wanda Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi wa jagora sun tafi gaban gidan gwamnatin suna zanga-zanga a baya bayan nan.

Sun bukaci shugaban kasar da suke zargin yana bannatar da kudaden ‘yan Nijeriya, ya tattara kayansa ya koma gida nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

A halin yanzu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana hutu a Birtaniya inda ya ce zai tafi domin likitocinsa su duba lafiyarsa.

Indai jama’a basu manta ba Buhari ya baro Nijeriya a dai-dai lokacin da kungiyar likitoci na kasar ke daf da shiga yakin aikin yi.

Labarai Makamanta