Zanga-Zangar Landan Adawa Ce Da Rashin Kunya Ga Buhari – Abba

An bayyana zanga-zangar da wasu ‘yan Najeriya mazauna Ingila suka yi wa Buhari a birnin Landan da cewar tsantsar adawa ce da rashin kunya wadanda suka yi Zanga-Zangar suka gwada wa Buhari.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba lokacin da yake tsokaci akan Zanga-Zangar a yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Kaduna.

Abdullahi Gambo Abba wanda ke riƙe da Sarautar Jakadan Hayin Banki Kaduna ya ƙara da cewar, abin da wadannan ‘yan Najeriyar suka yi rashin kunya ce ba adawa ba, dalili kuwa ita adawa ana yin ta ne ta hanyar suka mai ma’ana, amma bisa ga abin da ya faru a Landan rashin kunya ce, yadda aka samu wasu na ta antaya wa shugaban zagi.

Dangane da batun yajin aikin da likitoci suka tsunduma ciki a halin yanzu kuwa suna sukar lamirin Shugaban kasa da gaza gyaran Asibitocin gida, Gambo Abba yace shima akwai damuwa dalili kuwa Asibitoci a kasar nan sun daɗe a halin da suke ciki kusan tun lokacin da kasar ta koma bin tafarkin dimukuraɗiyya a shekarar 1999, amma me yasa Likitocin basu taɓa aiwatar da yajin aiki akan gyaran Asibitoci ba sai a zamanin wannan gwamnati, kamar Buhari ne farkon shugaba a kasar, lallai akwai rina a kaba.

Jakadan Hayin Banki ya kuma soki lamirin masu kokarin dangata halin da tsaro ke ciki a Najeriya da siyasa da cewar su guji hakan, lallai ne a fili yake tsaro ya shiga wani hali a ƙasar nan, kuma akwai gazawar Gwamnati ta wannan fuska.

Labarai Makamanta