Zanga-Zangar Da Aka Yi Wa Buhari Farmaki Ne Ga Arewa – Matawalle

Mai girma Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Muhammad Bello Matawallen Maradun ya kwatanta zanga-zangar da wasu ‘yan Najeriya mazauna London suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin hari ne aka kaiwa arewa.

A cikin wata takarda da aka fitar ranar Alhamis wacce Matawalle ya tura ya bayyana zanga-zangar a matsayin al’amari da wasu suka dauki nauyi, kuma wadanda suka shirya basu da wayewa.

Ya kuma ja kunne akan kaiwa ‘yan arewa hari da kuma sana’arsu a kudu. “Na yi Allah wadai ta yadda kullum ake nuna tsana ga dan arewa kuma hakan ya zarce har suka kaiwa Buhari hari saboda masu zanga-zangar ba zasu iya boye tsana da hassadar da suke yi wa ‘yan arewa ba.

“Duk yadda suke fushi, abinda suka yi bai dace da dabi’a da wayewa da mutunci ba. Yanzu haka tsanar shugaban kasa da arewa tana kara yawaita a garesu.

Gaskiya yin hakan bai dace ba ko kadan kuma daga masu zanga-zangar har masu daukar nauyinsu basu da wata daraja. “Na tabbatar da shugaban kasa dan kudu ne ba zasu yi masa haka ba, kuma sun yi hakan ne musamman don su wulakanta shugaban kasa sakamakon ganin yawan ‘yan Najeriyan da suke zama a London.

Labarai Makamanta