Zan Yi Wa ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Dalibai Ruwan Bama- Bamai – El Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyyana cewa ya shirya yiwa ‘yan Bindigar da suka sace daliban kwalejin Ganduj Daji dake Afaka Kaduna ruwan bamabamai koda kuwa za’a kashe wasu daga cikin daliban da suka sace.

Yace Jihar Kaduna na fuskantar yaki ne dan haka ko da an kashe daliban, sadaukarwace wadda dole a yita dan maganin matsalar.

Gwamnan ya kara da cewa, kwanaki 2 bayan da aka sace daliban, sojojin sama dana kasa su sanar dashi cewa, sun gano inda daliban suke kuma sun kewayesu, yace sun shirya afkawa ‘yan bindigar duk da sun san cewa za’a kashe wasu daga cikin daliban amma dama haka yaki yake, dole sai an yi sadaukarwa.

Yace suna cikin wannan shirine kawai sai ‘yan Bindigar suka sulale daga wajan. Ya bayyana hakane a wata ganawa da aka yi dashi ta kafar sadarwar zamani da wata coci ta shirya kan ci gaban Africa.

Labarai Makamanta