Zan Yi Takarar Zama Dan Majalisa A 2023 – Rarara

Shahararren mawaƙin siyasa Dauda Adamu Kahutu (Rarara), ya bayyana cewa maganar da ake yawo da ita ta batun tsayawarsa takarar zama ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya mai wakiltar Ƙananan Hukumomin Bakori da Ɗanja da ke Jihar Katsina gaskiya ce.

Mujallar Fim ta ce Rarara ne ya tabbatar mata da hakan a wata hira da ta yi da shi.

Mawakin ya ce kwanan nan zai tsunduma zagaya jihohin Nijeriya domin nuna irin ayyukan da ya gano Buhari ya yi.

Ya ce, “Idan Allah ya sa na kammala wannan aikin da ke gabana, to zan tsaya takarar ɗan Majalisar Tarayya na Ƙananan Hukumomin Bakori da kuma Ɗanja.

“Idan kuma wannan aiki ya sha gabana, sai kuma a duba batun nan gaba.”Article share tools

Labarai Makamanta