Zan Yi Takarar Gwamnan Kaduna A PDP – Shehu Sani

Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce zai nemi takarar gwamna a jihar tasa ƙarƙashin jam’iyyar adawa ta PDP a babban zaɓen 2023.

Sanatan wanda aka gani kwatsam a babban taron jam’iyyar na Asabar, ya kwana biyu da bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PRP amma ya ƙi fayyace inda ya koma.

Tsohon ɗan gwagwarmayar ya faɗa wa BBC cewa mutane ne ke neman ya tsaya takara “amma gara mutum ya nemi muƙamin da zai iya sauya duk abin da aka yi”.

“Hakan yana nufin na koma PDP a hukumance,” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko yana da niyyar takara a PDP, sai ya bayar da amsa da cewa: “Mutane na kira mu tsaya takara kuma za mu nema a wajen Allah. Takarar gwamman Kaduna zan yi.”

Labarai Makamanta