Zan Tona Asirin Masu Daukar Nauyin ‘Yan Bindigar Jihata A Badi – Gwamnan APC

Labarin da muke samu daga Owerri babban birnin Jihar Imo na bayyana cewar Gwamna Hope Uzodimma ya sha alwashin bayyana sunayen wadanda ke da hannu wajen kai hare-hare a jihar Imo da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

PM News ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne a wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar fadar gwamnatin jihar makon da ya gabata.

Ya yi bayanin cewa wasu mutane 18 ne da jami’an tsaro suka kama kwanan nan kan kashe kansiloli biyu a jihar, suka bayyana sunayen wadanda suke haddasa rashin tsaro, a faɗin Jihar.

Ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da za ta iya don tabbatar da cewa jihar ta zauna lafiya. Gwamna Uzodimma ya kara da cewa duk wanda ke karfafa aikata laifuka a jihar, komai girmansa, to zai fuskanci fushin doka.

“Bari in bayyana cewa, an kashe wadannan kansiloli biyu kwanan nan, kuma an kama wadanda suka kashe su kuma sun amsa abin da suka aikata. “Kada ku ji tsoro. Idan har nine Gwamna a jihar nan, za su fuskanci fushin doka.

Muna da shaida kan wadanda ke da hannu a lamarin rashin tsaro bisa bayanan da aka samu daga wadanda ake zargi. “Zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2022, lokacin da zan gudanar da taron masu ruwa da tsaki na Imo, zan fitar da sunayensu daya bayan daya tare da shaidar rawar da suka taka.”

Labarai Makamanta