Zan Taimaki Matasa Wajen Samun Mukamai A APC – Buhari

Mai girma Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari rana Jumu’a, ya tabbatar wa matasan APC cewa zai goyi bayan zakakurai daga cikinsu su ɗare manyan muƙamai a babban taron APC dake tafe a ranar 26 ga watan Fabrairu.

Kazalika Buhari ya umarci shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Farfesa Ibrahim Gambari, da Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, su tabbatar an saka matasa masu hazaka a gwamnatinsa.

Bayan haka Shugaba Buhari ya roki matasan APC su yi aiki tukuru wajen tabbatar da jam’iyya ta cigaba da rike kujerun gwamnonin jihar Ekiti da Osun da zaɓen su ke tafe cikin 2022.

Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar haɗa kan matasan jam’iyyar APC a fadarsa Aso Villa dake Abuja, ranar Jumu’a.

“Zan goyi bayan zakakurai kuma waɗan da suka shirya daga cikin matasa, waɗan ke neman wasu mukaman jam’iyya a babban gangami dake tafe.”

“Yana daga cikin manufofin da muka sa a gaba mu tabbatar da gina jam’iyya mai kwari da dogon zango ta hanyar mutanen da zamu miƙa wa ragamar tafiyar da ita.” “Ya kamata a kara karfafa wa mutane masu hazaka da juriyar aiki wajen tabbatar da gina hanya mai ɗorewa.”

Labarai Makamanta