Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Yobe, Mala Buni ya maida wa sanata Kabiru Marafa da zazzafar martani inda ya ce marafa karamin kwaro ne da ‘bai wuce ya murkushe shi ba.’
An ruwaito labarin korafin da Kabiru Marafa yayi kan ci gaba da shugabancin jam’iyyar APC da gwamnan Yobe Mala Buni ya ke yi cewa ya saba wa dokar kasa da ta jam’iyyar APC.
Marafa ya ce babu inda dokar kasa ko kuma na jam’iyya ta ba wanda ke da mukamin gwamna ya rike kujerar siyasa kuma ” A dalilin haka tabbas zan garzaya kotu domin a fassara min hujjar da ya sa Mala Buni ke rike da kujerar shugaban jam’iyyar APC duk da yana gwamnan jiha.
” Ba za ta sabu ba, dole sai Mala Buni ya sauka daga kujerar shugaban jam’iyyar APC ko ya ki ko ya so. Zan garzaya kotu domin a tabbatar masa cewa karya doka ce zaman sa shugaban jam’iyya bayan kuma yana rike da mukamin gwamnan jiha.
“Wane ne ya zabi Buni da kwamitinsa? A wani babban taro ko majalisa? Ni dinnan da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da wasu ‘yan APC muka yi ruwa mu kai tsaki har Buni ya zama sakataren jam’iyyar a shekarun baya.
” Sannan kuma zamu bukaci lallai menene doka tace game da duka abubuwan da ya gudanar a tsawon lokacin da yake shugabancin jam’iyyar har zuwa yanzu.
” A cire wannan mutumin daga shugabancin jam’iyyar APC tun da wuri kafin ya yi ragaraga da ita, na fito aikin ceto ne.
Martanin Mala Buni
Kakakin shugaban Jam’iyyar APC, gwamman jihar Yobe, Mala Buni, Mamman Mohammed ya bayyana cewa ruwa ne ya kare wa dan kada yasa Marafa ya ke yabo maganganun da ba su da da kai bare gindi’.
Mohammed ya ce kayar da Marafa da aka yi a zaben deliget da aka yi wanda ya fadi kasa warwas shine ya sa yake ta yi wa mutane kumfar baki ya na zazzaro ido wai za shi kotu, toh ” Ya sani shi karamin kwaro ne”.
” Ruwa ne ya kare wa dan kada, ta kare wa Marafa a siyasa. Da ga abu ya same shi sai ya ce wane ne yayi masa ba daidai ba. Maimakon karika watangaririya a gari kana ife-ife ka hutacce da kanka kawai ka rika garzaya wa kotu ne.
You must log in to post a comment.