Zan Sauya Alkiblar Najeriya Idan Na Zama Shugaban Kasa – Kwankwaso


Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya yi alkawarin habaka tattalin arzikin kasar tare da sake fasalin Nijeriya idan aka mara masa baya a zaben shekarar 2023

Kwankwaso ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Liberty a Abuja ya kuma yi alkawarin sanya ilimi a matsayin farko a gwamnatinsa, idan ya yi nasara a zaɓen 2023.

Tsohon gwamnan jihar Kanon ya kara da cewa gwamnatinsa za ta samar da yanayi mai kyau ga kananan ‘yan kasuwa ta hanyar bunkasa yanayin kasuwancinsu tare da karfafawa mata da matasa gwuiwa dan damawa dasu aharkokin kasuwanci.

“Za mu ba da fifiko kan ilimi, zamu magance matsalar rashin tsaro da yanayi mai kyau dan haɓaka kasuwanci”

“Da wadannan matakan zamu samawar da ƴan kasa damarmaki haɗi da bude musu hanyoyin bunkasa tattalin arzikinsu.

“Za mu inganta abubuwan da ake samarwa a gida da kuma tsarin shigo da kayayyaki da samar da ayyukan yi A cikin gida. Wadannan da ma wasu da dama su ne batutuwan da zamu maida hanakali a kai.

“Kullum muna tashi mu ga ƙudin kasar nan darajarar sa tayi ƙasa, kullum ƙudin kasashen waje kara hawa yak e. wannan na cikin abun da gwanati ta kamata ta kalla; amma ina, ku duba kuga yadda kullum tattalin arziki ke tabarbarewa”

A kan matsayin na sake fasalin kasa, Kwankwaso ya ce zai yi aiki kafada da kafada da Majalisar Dokokin kasa da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma, domin fara aikin sake fasalin tun daga tushe.

Ya yi nuni da cewa, tsarin nasa wanda nan ba da dadewa ba za a gabatar da shi ga jama’a, ya yi duba da yanayin da kasar nan ke ciki, tare da mai da hankali kan yadda halin da al’umma suka shiga dangane da harkokin mulki, ya kara da cewa dole ne Najeriya ta dawo da matakan da ta dauka domin daidaita lamarin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply