Zan Sadaukar Da Rayuwata Wajen Yakar ‘Yan Ta’adda – Matawalle

Rahotanni daga Gusau babban birnin Jihar Zamfara na bayyana cewar Gwamnan jihar Bello Muhammad Matawallan Muradun ya ce mutum 36 aka kashe a karamar hukumar Bukkuyum.

Cikin wata tattaunawa da BBC Matawalle ya ce sakamakon harin da aka kai a kananan hukumomin Anka da Bubukkuyum ya ziyarar gani da ido don tabbatar da irin ɓarnar da ƴan bindigar suka yi.

Ya ce yanzu haka suna da sunaye da bayanan mutanen da aka kashe ɗin.

Gwamnan ya ce daga Bukkuyum Anka zai wuce domin ya tabbatar da abin da rahotanni ke ambatowa cewa sama da mutum 200 aka kashe.

“Zan sadaukar da rayuwata zan bada raina gaba ɗaya wajen kawar da ‘yan ta’adda a jihar Zamfara”

Ya ce zai yi iya kokarinsa domin ganin cewa an mayar da duka wadanda suka gudu daga wadannan kauyuka zuwa garuruwansu nan da mako guda.

Labarai Makamanta