Zan Mayarwa Sanusi Sarautar Kano Idan Na Zama Gwamna – Abba Gida-Gida

Dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin tutar jam’iyar PDP a shekarar 2019 Abba Gida-Gida yace idan yaci zaben kujerar gwamnan Kano a zaben shekarar 2023 mai zuwa sai ya sake Nada tsohon sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi II a matsayin sarkin Kano.

Sannan yace dukkan sababbin masarautun da gwamnatin Kano karkashin Ganduje ta kirkira sai ya rushe su ya mayar dasu hakimai kamar yadda aka san su.

Abba Gida-Gida ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai a birnin Kano, dangane da kudirin da yake dashi na takarar gwamna a 2023.

Indai jama’a basu manta ba a shekarar bara ne gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tsige Sarki Muhammadu Sanusi ll daga sarauta bayan ya zarge shi da nuna goyon baya ga jam’iyyar PDP.

Labarai Makamanta