Zan Kunyata Malaman Kano Ranar Muƙabala – Kabara

Sanannen Malamin Darikar Ƙadiriyya a Jihar Kano AbdulJabbar Nasiru Kabara, ya bayyana godiya da jin daɗin shi dangane da ayyana ranar fafata muƙabala tsakanin shi da Malaman Kano, inda ya bayyana cewar babu shakka zai kunyata su.

Malamin a wata wasika da ya aikewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya ce zai halarci mukabalar kuma ya yi godiya ga gwamnan a kan damar da ya bashi domin kare kansa.

Idan za mu tuna gwamnatin jihar ta saka ranar Asabar, 7 ga watan Maris domin mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da sauran malaman jihar Kano.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano Malam Muhammad Garba, a wata takardar sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ya ce daga Sheikh Abduljabbar da malaman Kano duk an basu wasikar wacce ke bayyana ranar mukabalar.

Amma kuma Abduljabbar ya ce dukkan koyarwarsa da wa’azinsa yana yi ne don baiwa nagartar Annabi Muhammad kariya ba kamar yadda wasu mutane ke zarginsa ba.

Gamayyar Malaman Musulunci a Kano sun zargi AbdulJabbar da yin kutse cikin littafan addini da kuma yin karan tsaye ga fassarar karatun kamar yadda aka saba a tsawon zamani.

Labarai Makamanta