Zan Jagoranci Najeriya Kamar Yadda Tafawa Balewa Ya Yi – Atiku

Rahoton dake shigo mana daga jihar Gombe na bayyana cewar Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi alkawarin tabbatar da wuta daga madatsar wuta ta Dadin Kowa da ke jihar Gombe idan aka zabe shi a zaben 2023.

Atiku Abubakar ya bayyana aniyarsa ta bin sawun salon mulki da tsari irin na tsohon firayinministan Najeriya, marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, wanda ya sadaukar rayuwarsa wajen ciyar da ƙasa gaba, inda yace ‘yan Arewa maso Gabas za su samu alheri idan suka zabe shi a 2023.

Da yake magana a taron gangamin kamfen na PDP a jihar, Atiku ya ce dukkan hanyoyin da ke hada Gombe da Adamawa da Borno, da kuma hanyar da ke hada Gombe da Bauchi da Yobe duk za yi aikin gyara su.

“Bari na maimaita alkawarin da na dauka idan Allah ya sa kun goyi bayan PDP. Mun yi alkawarin karfafa ‘yan kasuwanku don inganta kasuwanci ta yadda za su fadada kasuwancinsu don matasanmu maza da mata. “Mun kuma yi alakawarin cewa, madatsar ruwan Dadin Kowa, wanda aka gina a mulkin PDP don samar da wutar lantarki da harkar noman rani za su fara aikin samar da wuta da noman rani matukar kuka goyi bayan gwamnatin PDP.”

Labarai Makamanta