Zan Gina Sabuwar Najeriya Idan Na Zama Shugaban Kasa – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar ɗan takarar Kujerar zama shugaban kasa a inuwar jam’iyya mai mulki ta APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yace da ikon Allah ‘yan Najeriya ba zasu yi da nasani ba idan suka zaɓe shi shugaban kasa a 2023.

Tinubu ya ba da wannan tabbacin ne a wurin gangamin yakin neman zaɓensa da ya gudana a Kaduna ranar jiya Talata.

Gangamin Kaduna somin taɓi ne na fara yakin neman zaben shugaban kasa na APC a shiyya mafi yawan kuri’u a Najeriya watau arewa maso yamma.

Da isarsa Kaduna ranar Litinin, Bola Tinubu ya zarce zuwa Birnin Gwari, ƙaramar hukumar da ta’addancin ‘yan bindiga ya fi addaba a jihar inda ya ganewa idonsa yadda yankin da kuma shan Alwashin magance matsalar tsaro idan ya lashe zabe.

Da yake jawabi ga dandazon mutanen da suka fito tarbansa, tsohon gwamnan jihar Legas din yace idan aka zaɓe shi a 2023, zai kawar da ‘yan bindigan daji daga doron duniya. Haka zalika ya ɗauki alƙawarin fifita hanyoyin rage zaman kashe wando, samar da aiki mai gwabi ga matasa da kuma haɓaka noma ta hanyar kafa hukumar kasuwanci.

“Muna godiya ga Allah SWT da ya kawo mu nan kuma muna gode muku da kuka ci gaba da goyon bayan jam’iyyar mu, ba zaku yi dana sani ba insha Allahu.” “Duk waɗan nan masu ta da ƙayar baya, masu garkuwa, masu kashe-kashe da suka hana Kaduna zaman lafiya da arewacin Najeriya ina tabbatar muku zamu kawar da su Insha Allah.”

Labarai Makamanta