Zan Gama Da Dukkanin ‘Yan Bindigar Najeriya – Magajin Ali Kwara


AHMAD MUHAMMAD KWARA shi ne magajin fitaccen mai farautar barayi a Nijeriya wato Alhaji Ali Kwara wanda ya shahara wajen yaki da ‘yan fashi da makami, sannan ya kasance kani ne a gare shi wanda suke uwa daya uba daya. A hirarsa da ‘yan jarida ciki har da wakilin Jaridar Leadeship Hausa KHALID IDRIS DOYA a wajen wani taron tunawa da marigayi Ali Kwara da Kungiyar Matasan Arewa ta shirya kan irin gudummawar da ya bayar wajen inganta harkokin tsaro. Ya tabbatar da cewa kwanan nan barayin daji za su tabbatar Ali Kwara da ya tafi, ya dawo. Ga tattaunawar:

Ya kake kallon wannan taron tunawa da dan uwanka Ali Kwara da aka shirya tare da bitar muhimman gudunmawar da ya bayar lokacin da yake raye? 

Gaskiya shi yayana a lokacin da yake raye ya yi ayyuka da dama kuma ya tsaya wa mutane da dama, ya taimaki al’umma kuma shi ma ya samimu goyon bayan jama’a manya da kanana. Don haka wadanda suka shirya wannan taro sun kyauta mana domin mu suka karrama, shi kam ya yi nasa ya tafi ya bar mu da kewa da darussa masu yawa da muka koya daga wurinsa, addu’o’in da aka masa mun tabbata za su isa gareshi. Mun gode da shirya wannan taron.

Alhamdulillahi, tun da marigayi ya rasu ni ne aka bai wa ragamar yin wannan tafiya, kafin mu fara sai da muka nemi izinin manya a kasa kamar shugaban kasa da kuma shi Babban Sufeto Janar na ‘yan Sanda, mun je mun zauna da su kuma sun ba mu izinin a hukumance na in ci gaba daga inda shi wana ya tsaya. Tun lokacin cikin shekara guda da rasuwarsa, mun yi kokari sosai wajen yin ayyuka da yawa tare da jami’an tsaron da muke aiki tare kuma an sami nasarori, ba wai a  Jihar Bauchi kawai ba har ma da wadansu jihohin, domin mun shiga wasu yankuna a jihohin Kaduna da Katsina, kuma duka Allah ya ba mu nasarori na kama barayi tare da mikasu ga hukumomi.

Sakamakon aikin hadin gwiwa tsakaninmu da hukumomin tsaro, ana samun ci gaba sosai wajen inganta zaman lafiya, don shi wannan aiki kamar yadda marigayi yake fada a kullum aiki ne na taimaka wa jami’an tsaro don kama masu aikata laifuka, muna tare da su, su ne suke yin aikinsu, mu dai muna taimaka musu ne. Muna tare da su jami’an ‘yan sanda da muke aiki da su a ko’ina, gida da waje, kuma lokacin da muka zauna da Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda ya ba mu cikakken goyon baya sosai, ya ce duk jihar da muka je za mu yi aiki za a kara mana karfin jami’an tsaron da za mu shiga daji da su mu yi aikin farautar barayin, idan muka kammala kuma mu dawo da wadanda aka hadamu  aiki da su gida. Ka ga muna aiki da su ba wata matsala suna ba mu goyon baya sosai muma muna taimakonsu.

Wasu irin goyon baya kuke samu daga gwamnatocin jihohin idan kuke shiga farautar barayi?

Alhamdulillahi, su ma suna ba mu goyon baya da hadin kai sosai, duk da cewar shi aikin da mu ke yi akwai sirri a ciki,  za mu iya samun bayanin masu laifi, mu shiga gari mu yi aikinmu har mu fito ba wanda ya sani sai dai bayan mun kammala, kuma wani lokaci kamar yadda wasu gwamnatocin jihohi ke neman gudumawarsa lokacin yana raye don a yaki ‘yan fashi da makami, muna samun hadin kai kan haka. Ka san muma muna amfani da wadanda ke ba mu bayanai kan maboyar barayi, a wani lokaci suma barayin kamar sace musu muke yi, ko mu yi musu kwanton bauna mu ritsasu sannan mu kamesu. Shi ya sa sai mu shiga mu yi aiki mu fita ba wanda ya sani.

Shin kana amfani da irin salo da dabarun kama barayin da yayanka ke amfani da su?

Gaskiya ina yi kuma ka san kafin ya rasu ya bar masu ba da bayanai kan maboyar barayi  wadanda muke kira (informants) a jihohi da dama, wadanda da su barayi ne sun bar sata sun koma suna ba shi labarai, wadannan mutane har yanzu muna tare da su, mun zauna da su bayan rasuwarsa na shaida musu cewa Ali Kwara ya tafi amma ya dawo saboda haka aikin da a baya yake yi da ku mu ci gaba, duk inda suka ji wani labari mai kyau sukan ba mu bayanai, mu kuma mu kan je mu yi abin da ya kamata, yanda yake yin tsarinsa da dabarunsa haka muke yi.

A halin yanzu ana fama da matsalar ‘yan fashin daji masu dauke da makami, gungun barayi masu sata da garkuwa da mutane da suke zaune cikin dazuzzuka, ko kuna wani yunkuri na shiga cikin dazuzzukan domin yaki da barayin?

Gaskiya mun yi sosai musamman a yankinmu na kasar Katagum ba wanda zai ce maka akwai wani mai sata da garkuwa da mutane ko gungunsu a cikin dazuzzukanmu, mun yi yaki da su kuma Allah ya taimakemu mun kore su daga ciki. Ka san an ce yanda kyan mutum ya fara daga gida, don haka daga gida na fara kuma mun fita, don yanzu haka zancen dana ke maka muna kan aiki cikin dajin Jihar Katsina, muna iya kokarinmu a wajen daga nan kuma za mu yi Jihar Zamfara da ikon Allah.

Amma har yanzu akwai dajin Lame Burra a cikin Jihar Bauchi shi ma ana koken cewa baki miyagun barayi sun buya adajin ko ka kai samame wurin?

Gaskiya ba mu shiga cikin wannan dajin ba, amma cikin makon nan mun yi magana kan wannan dajin na Lame Burra da jami’an gwamnati. Kuma zamu shirya masa domin mu ba da gudummwa a tsarkake dajin cikin ikon Allah.

Daga lokacin da ka fara jagorantar tawagar nan mutum nawa kuka kama?

Mun kama da yawa, a karamin lissafi mun kama barayin fiye da 50 kuma ka san kamar yadda marigayi yake yi in mun kama barawo muka tatse bayanansa sai mu bar wa jami’an’yan sanda domin su kai shi ya fuskanci hukuncin irin laifuffukan da ya aikata.

Shi marigayi ya sha kokawa cewar zai kama barawo sai ‘yan sanda ko kotu su sake su ko kai ma ka samu wannan matsala zuwa yanzu?

A yanzu dai ni ban samu irin wannan matsalar ba, muna samun goyon baya sosai don duk wadanda muka kama in dai mu muka ba su an yi musu hukunci, jami’an ‘yan sanda da kotu duk suna ba mu goyon baya saboda cikin wadanda na kama babu wani a waje duk suna tsare a gidan gyara halinka.

Wani shawara za ka bai wa al’umma?

Lallai ba abin da muke nema a wurin jama’a kamar goyon baya da hadin kai da addu’o’i. Muna bukatar addu’a kwarai a wurin jama’a, su kuma barayi muna shawartarsu su tuba su dai na don ba abu ne mai kyau ba, masu magana sun ce rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya saboda haka ko su tuba ko wata rana Allah zai ba mu nasara a kansu mu kamasu a hukuntasu da ikon Allah.

Labarai Makamanta