Zan Dora Daga Inda Buhari Ya Tsaya – Tinubu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress APC na kasa, ya ce zai tsaya takarar shugabancin kasa a 2023 domin dora ƙasa bisa ginin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya faro.

Bola Tinubu, wanda ya ziyarci Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari domin tattaunawa kan burinsa na siyasa a ranar Litinin, ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugaban.

“Ina da kwarin guiwa da hangen nesa, da ikon yin mulki, gini kan ginshikin shugaban kasa, da kuma inganta Najeriya wanda na yi kamar hakan da jajircewa a jihar Legas.”

“Bisa ga haka ina ƙara tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ina da da koshin lafiya da ikon juya abubuwa yadda ya kamata domin kai wa ga mataki na gaba.

Labarai Makamanta