Zan Dawo Da Tsaro Cikin Hayyacinshi – Sabon Shugaban ‘Yan Sanda

Sabon Shugaban ‘yan sandan ya yi alkawura da dama na sakewa da karfafa rundunar ‘yan sandan Najeriya a daidai lokacin da satar mutane, kisan rashin tunani, da duk wasu nau’ikan aikata laifuka ke addabar kasar.

An ruwaito cewa shugaban ‘yan sandan ya tabbatarwa da’ yan kasar cewa wa’adinsa zai ba da fifiko wajen kafa ‘yan sandan jiha a matsayin babbar dabarar yaki da kawar da ta’addanci.

Da yake bayyana cewa zai ci gaba daga inda wanda ya gada ya tsaya, Baba ya ce: “Za mu ci gaba da aiki da shi.

Wanda ya gabace ni ya tafi muna a wani mataki na fari, mun fara shi amma ba mu yi nisa ba, saboda haka, duk hanyoyin an tsara su kuma za mu ci gaba da shi tare da hadin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki.”

Sabon Shugaban ‘yan sandan ya ce za a samu ci gaba abin yabawa a yanayin tsaron Najeriya don haka, ya yi kira ga kowa da kowa da su taimaka wa ‘yan sanda yayin da suke tunkarar miyagun laifuka a karkashin jagoranci na hakika.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zai sa fashi da makami da ta’addanci su zama tarihi a cikin kasar.

Sauyi a tsarin aiki IGP Baba ya bayyana cewa za a samu gagarumin sauyi a tsarin gudanar da ayyukan rundunar wajen magance rashin tsaro a fadin kasar.

Labarai Makamanta