Zan Cire Tallafin Mai Bai Da Amfani Ga Talaka – Tinubu

Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya ci alwashin cire tallafin man fetur idan ya ci zaɓen shugaban ƙasa da za a yi a watan gobe.

Tinubu ya ce zai cire tallafin man ne sabo da masu kuɗi ne ke amfanar sa ba talakawan ƙasa ba.

Da ya ke zantawa da gidan rediyon Freedom Radio ta wayar tarho, yayin da ya ke gudanar da ibadar Umurah a Saudiyya Tinubu ya ce tallafin man wata kafa ce ta asarar kuɗaɗe, inda ya ce idan ya hau mulki, zai karkatar da kuɗaɗen tallafin zuwa wasu hanyoyin da talakan Nijeriya zai amfana.

Ya ce abokan hamayyar APC duk sun razanar da irin shirin da jam’iyar ke yi na lashe zaɓen mai zuwa, inda ya nuna yaƙinin cewa shi zai lashe zaɓen.

Labarai Makamanta