Zan Ceto Sauran ‘Yan Matan Chibok Da Kaina – Zulum

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ce za za a ceto sauran ‘yan matan Chibok da ma sauran mutanen da aka sace daga jihar cikin koshin lafiya.

Zulum ya fadi hakan ne a cikin wani bayaninsa na cikar shekara bakwai da mayakan Boko Haram suka sace daliban na makarantar mata ta Chibok lokacin da suke gab da rubuta jarrabawarsu ta karshe.

Duk da cewa an sako wasu daga cikin daliban to amma har yanzu akwai da dama wadanda suka rage a hannun kungiyar ta Boko Haram.

Zulum ya ce a matsayinsa na uba, yana jin takaicin kuncin da iyayen ke ciki tsawon shekara bakwai yaransu na hannun ‘yan bindiga.

Ya bukaci mutane su taimaka da addu’o’i ga wadanda aka sace da kuma fatan dawowar zaman lafiya a jihar ta Borno

Labarai Makamanta