Zan Bude Iyakokin Najeriya – Buhari

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya bada sharadin bude iyakokin kasar nan don barin kaya su shigo daga kasashe masu makwabtaka.

Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a lokacin da ya hadu da Shugaban Burkina Faso Roch Marc Christian Kabore na kasar wanda ya kai masa ziyara a ranar Juma’a a gidan gwamnati da ke Abuja, kamar yadda Channels TV suka ruwaito.

A yayin ziyarar Buhari ya fada masa ceea “Babbar matsalarmu shine tsaro, shigo da makamai, harsasai da kuma kwayoyi,”.

Shugaban kasa Muhammad Buhari ya kara da cewa, “mun fahimci raguwa a ta’addanci tun bayan da muka rufe iyakokin kasarmu. Hakazalika, manonanmu yanzu na iya siyar da shinkafar gida tunda mun dena shigo da ta Turai wacce ke cika kasar nan.”

Ya sanar da bakon nasa cewa Najeriya ta yanke hukuncin sakaya iyakokinta ne saboda tabbatar da tsaron kasa .

Daga karshe: Buhari ya sanar da lokacin bude iyakokin kasar nan inda yace bude iyakokin kasar nan ya dogara ne a kan rahoton kwamitin bangare uku da ya hada da gwamnatocin Najeriya, jamhuriyar Benin da jamhuriyar Nijar Yace zaa bude in komai ya daidaita.

Yace “Zanyi aiki da gaggawa matukar na samu rahoto,” – inji Shugaba Buhari.

Daga karshe dai Shugaban Burkina Faso ya nemi Shugaba Buhari da ya kara duba matsayarsa.

Related posts