Zan Ƙauracewa Kaduna Da Zarar Na Kammala Mulki – El Rufa’i

Mai girma Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa kayanshi a ɗaure suke da zarar ya kammala wa’adin mulkinsa, zai tattara yanasa yanasa ya bar Jihar Kaduna gaba ɗaya.

Gwamna El Rufa’i ya yi wannan furuci ne a yayin wata tattaunawa da aka yi dashi a kafafen yaɗa labarai dake Jihar Kaduna a tsakiyar Mako.

Malam Nasiru El Rufa’i ya ƙara da cewar a tarihin rayuwarshi ya mallaki gida daya ne kawai wanda ke yankin Unguwar Sarki da ke cikin garin Kaduna saboda haka babu wani abin azo a gani da ya mallaka a Kaduna wanda zai kawo mishi tsaiko da zarar ya kammala karshen wa’adinsa a shekarar 2023.

Gwamnan ya ƙara da cewa nan ba da dadewa ba gwamnatinsa za ta rage ma’aikata daga cikin tsarin biyan albashi na jihar, kama daga ma’aikatan jiha har ya zuwa na kananan hukumomin Jihar, domin samun daidaito wanda ya dace.

Gwamnan ya kuma kara da cewa baya ga ma’aikatan gwamnati zai kuma rage yawan wadanda ya nada a mukaman siyasa, wannan ya zama dole mu aikata shi, babu gudu babu ja da baya.

“Bana satar kudaden gwamnati, bawai muna satar kudaden gwamnati bane don gina gidaje. Ina da gida ne a Unguwar Sarki kuma har zuwa yau shi ne gida daya tilo da na mallaka a Kaduna saboda bayan mulki na, ba zan zauna a Kaduna ba. Don haka, ba zan kara wani gida a jihar ba,” inji shi.

“Gwamnatin jihar ba za ta biya albashin mutanen da ba sa aiki ba, saboda haka, lamarin zai shafi ma’aikatan da basu cancanta ba da wadanda ke sama da shekaru 50 ciki har da wadanda ma ba sa zuwa aiki a kai a kai kuma duk da haka ana biyansu albashi.”

Game da wadanda aka nada a mukaman siyasa, ya ce, “Muna duba yiwuwar rage nade-naden mukaman siyasa ne saboda idan ka rage wasu ka kasa rage naka, hakan zai zama rashin adalci. Tabbas za mu bincika mu rage wasu daga cikinmu a zahiri, tuni mun fara aiwatar da tsarin.”

Labarai Makamanta