Zamu Zama Gatan Almajirai A Kasar Nan – Gwamnonin Borno Da Yobe

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana cewa ba za su kori duk wani almajiri da ba dan asalin jihar ba, maimakon haka za su yi gyara ne a harkar ta almajiranci, saboda su ma yara almajiran ‘ya’yansu ne.

Gwamna Buni ya kara da cewa jihohin Borno da Yobe cibiyoyi ne na neman ilmin addini a tarihance, don haka gwamnatinsa ta shirya yi wa harkar almajiranci kwaskwarima.

Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan, Gwamnatin jihar Borno ma na tuna cewa ba za ta kori almajirai daga jihar ta ba, maimakon haka za ta kawo gyara ne a harkar almajirancin, domin jihar Borno cibiya ce ta karatun allo.

Related posts