Zamfara: Za A Kashe Miliyan 400 A Tallafin Karatun Dalibai

Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da fitar da kuɗi har naira miliyan 400 domin biyan ɗalibai ‘yan asalin jihar tallafin karatu na zangon shekarar 2020/2021.

Tallafin ya shafi ɗalibai ‘yan asalin jihar ta Zamfara dake karatu a cikin jihar da ma waɗanda ke karatu a wasu makarantun ƙasar nan.

Wannan na daga cikin wani jawabi dake ɗauke da sa hannun Yusuf Idris, Daraktan yaɗa labaran gwamnan, wanda aka rarraba ga manema labarai a Gusau babban birnin Jihar.

Ya ƙara da cewar ƙarkashin zangon karatu na 2020/2021, gwamnan ya amince a fitar da miliyan 186.6 don biyan ɗaliban likitanci ‘yan asalin jihar da a yanzun suka shiga shekara ta biyu a karatunsu a ƙasar Sudan.

Hakanan kuma Matawalle ya amince a fidda kuɗi miliyan 24.5 don biyan ɗalibai 25 da gwamnatin ke ɗaukar nauyi a ƙasar Indiya. Kuma ya amince da fitar da miliyan 56.4 ga ɗaliɓan dake karatu a Cypros.

A cewar daraktan yaɗa labaran gwamnan: “Bayan gano gaskiyar lamarin bashin da ɗaliban jihar ke bin gwamnati na tallafinsu a jami’ar Al-hikmah Ilorin, jihar Kwara da jami’ar Crescent dake Abeoukuta, jihar Ogun, gwamnan ya bada umarnin fitar da Naira miliyan 70.”

Gwamnan ya kuma amince da biyan miliyan 19 ga ɗaliban dake karatun lauya na zangon karatun da ya gabata, 2019/2020. Ya ƙara da cewa gwamna Matawalle ya bada umarnin fara tantance ɗalibai ‘yan asalin jihar dake karatu a makarantun gaba da sakandire a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Labarai Makamanta